17 Mayu 2022 - 19:26
Iran :Ya kamata Amurka Ta Rika Mutunta Yancin Kan Sauran Kasashen Duniya

Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saed Khatib zade shi ne ya furta hakan a lokacin da yake mayar da martani kan wasu kalamai na tsoma baki da takwaransa na Amurka Ned price yayi game da wasu zanga-zangar da aka yi a baya- bayan nan a wasu biranen a kasar Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A cikin ganawar da ta yayi da manema labarai ya fadi cewa irin wannan farin cikin da Amurka ta nuna fiye da haddi yana nuna cewa matakin da gwamnatin iran take dauka na kare Tattalin arziki da jin dadin Alummarsu ne ke jefa Amurka cikin damuwa

A cikin bayanan da ya wallafa a shafinsa na twiter kakakin Ma’aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price yayi kokari kautar da hakikanin dalilan da yasa wasu gungun mutane suka yi zanga-zangar a iran zuwa wani abu na daban da bashi da kamshin gaskiya

Yace masu zanfa zangar na kasar iran suna da hurumin neman hakokinsu, Alummar iran suna da hakkin neman Karin bayani daga ayyukan da gwamnati ke yi, don haka muna goyon bayan hakkinsu na yin zanga zangar lumana da bayyana albarkacin bakinsu a fili da kafafen sadarwa na zamani ba tari da tada tsoro ko tada rikici ba.

342/